A hirar shi da Muryar Amurka, Magatakardan kungiyar mamallaka gidajen rediyo da talabijin masu zaman kansu da Gremah ke shugabanta kafin rasuwarsa, Lamine Souleyman, ya bayyana rawar da marigayi Gremah Boucar ya taka a ci gaban aikin jarida.
Bisa ga cewar shi, an zabi Gremah Boucar a matsayin shugaban kungiyar na farko sabili da kwarewar shi da kuma jajircewa wajen ganin an mutunta ‘yan jarida an kuma sakarwa kafofin sadarwa masu zaman kansu kota su gudanar da ayyukan su ba tare da tsangwama ba.
Ya bayyana cewa, Gremah ba ya goyon bayan duk wata shawara in ba abinda zai kawo ci gaban aikin jarida ba ne. Ya ce Grema ya taka kyakkyawar rawa a kwato ‘yancin kafofin watsa labarai masu zaman kansu.
Daga Gremah na koyi yadda ake kare aikin jarida, da hakin ‘yan jarida, da kuma hakin kafofin watsa labarai.
Malam Lamani ya ce a cikin shekaru goma sha biyar da ya shafe yana aiki da Gremah, ya sami amfani sosai a “kan yadda ake kare aikin jarida, da hakin ‘yan jarida, da kuma hakin kafofin watsa labarai.”
Ba faduwa ba ne matsala, faduwa a gaza tashi ne matsala"
Shi ma a nashi bayanin, Chitou Maman dan majalisar dokokin kasa wanda jam'iyarsu daya da Gremah Boukar, ya bayyana shi a matsayin mutum mai hakuri. Bisa ga cewarshi, Gremah yana yawan cewa, “ba faduwa ba ce matsala, faduwa a gaza tashi ne matsala”.
Issouf Mammne, daya daga cikin ma’aikatan radio Amfani na farko a Yamai, ya bayyana salon shugabanci da rayuwar marigayi Gremah Boucar da ya ce yana da saukin kai. Bisa ga cewar shi, wani lokaci ana kasa banbance ma’aikatan gidan radiyon da shi mai gidan, kasancewa yana mu’amala da su irin ta aboki da aboki ba shugaba da ma’aikaci ba. Ya kuma bayyana Gremah a matsayin malaminsa a aikin jarida da ya ce shi ne ya koya mashi duk abinda ya sani a aikin jarida.
Tarihin Marigayi Grema Boucar
Marigayi Gremah Boucar ya bada takaitaccen tarihin rayuwarsa a wata hira da gidan Radio Amfani inda ya bayyana cewa, ya sami karfin guiwa da kuma sha’awar kafa jarida mai zaman kanta ne daga kasashen duniya da dama da ya ziyarta.
Huldar Grema Boucar da Tashohin Kasashen Ketare
Paula Caffey jami’ar hulda da kafofin watsa labarai na kasashen ketare ta Muryar Amurka ta bayyana jimamin rasuwar Alh Gremah Boucar da ta ce yana daya daga cikin shugabannin kafofin sadarwa masu zaman kansu Muryar Amurka ta dade tana hulda da su.
A na shi bayanin, Shugaban Sashen Hausa, Aliyu Mustapha Sokoto wanda ya shafe kimanin shekaru talatin yana hulda da marigayi Gremah, ya yaba kwarewar aiki da kuma gwaggwarmaya da marigayin ya yi a fannin aikin. Ya bayyana Boucar a matsayin manuniyar aikin jarida, kuma daya daga cikin ‘yan jarida da su ka fi aiki da kusan dukan ma’aikatan Sashen Hausa wanda kuma banda Sashen Hausa, ya bada gagarumar gudummuwa ga Sashen Faransanci.
A shekarar alib da dubu tara da casa’in ta dakwas, wata kungiyar da ke kare ‘yancin ‘yan jarida a nahiyar Afrika ICJ ta ba Gremah Boucar lambar yabo sabili da jajircewarshi da kuma gwargwarmayar da ya sha da mahukunta da ya kai ga kama shi.
Kafin rasuwarsa, Gremah Boucar wanda ya fara da kafa jarida mai zaman kanta da suna Amfani, ya mallaki gidajen radiyo da kuma talabijin. Ya kuma shafe sama da shekaru 40 yana aikin jarida.
Saurari shirin A Bari Ya Huce na musamman da aka karrama Gremah: