Gwamnonin Kaduna da Sokoto ne kawai ya zuwa yanzu su ka nada kwamishinoni daga cikin gwamnoni 7 na shiyyar arewa maso yammacin Najeriya, yayin da gwamnan Bauchi ne kawai ya nada kwamishinonin sa daga cikin jihohi 6 na shiyyar arewa maso gabashin Najeriya.
A shiyyar arewa ta tsakiya kuwa, gwamnonin Kwara da Nasarawa da kuma Filato na daga cikin gwamnonin da ba su fitar da jerin kwamishinonin su ba har yanzu.
Gwamnan Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya ce har yanzu yana nazarin mutanen daya kamata ya nada a mukaman kwamishinoni, kuma mambobi a majalisar zartarwa ta jihar.
Gwamana Ganduje ya kuma kara da cewa wa’adinsa na biyu zai sha banban da wa’adin mulkinsa na farko, kuma zai dawo da wasu daga cikin tsoffin kwamishinonin sa wasu kuma ba za su dawo ba, za su fitar da sunayen su nan bada jimawa ba.
To sai dai masu sharhi a fagen siyasar Najeriya na ci gaba da tsokaci dangane da illar da wannan jinkiri mika ‘iya haifarwa ga tsarin tafiyar da gwamnati.
Malam Kabiru Sufi masanin kimiyyar siyasa ne kuma mai koyar da wannan fanni a kwalejin share fagen shiga jami’a ta Kano, ya ce a dokance akwai iya adadin kudaden da gwamnoni ya kamata su kashe ba tare da majalisar zartarwa ba, kuma hakan yana kawo nakasu ga shugabanci.
Sufi ya kara da cewa yana fatan idan aka fitar da kunshin majalisu ya zama kwalliya ta biya kudin sabulu ba ya kasance ace an fitar da mutanan da ba za’a ga ingancinsu ba.
Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari daga Kano:
Facebook Forum