Jami’an dake tafiya tare da Clinton sun ce ta fadawa shugaba Jonathan da manyan jami’an tsaron Najeriya cewa a shirye Amurka ta ke ta taimaka wajen horas da ‘yan sanda da rundunonin yaki da ta’addanci wadanda ke fafatawa da ‘yan Boko Haram. Ana dora wa kungiyar ta Boko Haram alhakin hare-hare da dama da kuma mutuwar mutane fiye da 600 a wannan shekara kawai, a kokarinta na kafa tafarkin shari’ar Musulunci a kasar mai mutane miliyan 160.
Kungiyoyin kare hakkin bil Adama sun ce kungiyar Boko Haram ta fi yawaita hare-hare a kan jami’an tsaro da na gwamnati, da gine-ginen gwamnati da kuma majami’un Kirista a wannan kasar da kusan al’ummarta rabi Musulmi en rabi kuam Kirista.
Ya zuwa yanzu dai, gwamnatin ta Najeriya ta kasa kawo karshen wannan zub da jini.
Har ila yau, Clinton ta roki gwamnatin Najeriya da ta kara zage damtse wajen nuna gaskiya da kawar da cin hanci da rashawa a wannan kasa dake cikin wadanda suka fi kaurin suna a duk duniya wajen cin hanci da wawurar dukiyar jama’a.
Sakatariya Clinton ta kai wata gajeruwar ziyara zuwa Jamhuriyar Benin, daga nan kuma ta doshi kasar Ghana inda a yau zata halarci jana’izar marigayi shugaba John Atta Mills.