Direban mai suna Mohammed Azam shi ne yake tuka shugaban Taliban Mullah Mansoor lokacin da harbin da jirgin ya kai ya fada kan motar a kudu maso yammacin yankin Baluchistan ya kashesu.
'Yansandan wani kauyen lardin Noshki inda harin na ranar Mayu 21 ya auku sun tabbatar jiya Lahadi cewa 'yanuwan Azam sun fara shirin kai kara gaba ta hanyar shigar da bayanan farko akan jami'an na Amurka.
Wani dan'uwan marigayin yace dan'uwansa mai 'ya'ya hudu bai yi wani laifi ba kuma shi ne kadai yake iya ciyar da iyalansa domin dukansu suna fama da talauci.
Ya cigaba da cewa dan'uwansa Azam bashi da alaka da kowace kungiyar ta'adanci kuma a matsayinsa na direban takasi ya kan dauki fasinjoji daga garin Taftan, garin da Pakistan tayi iyaka da Iran da kuma Quetta babban birnin Baluchistan.
Yace "ina neman adalci ta daukan mataki akan jami'an Amurka da suka yi sanadiyar wanna harin. Ban san sunayensu ba amma kafofin labaru sun ambatosu suna ikirarin su ne suka dasa bam din da ya kashe danuwana"
Wani lauya mai zaman kansa a Quetta, Tahir Hussain, ya shaidawa Muryar Amurka cewa iyalan mamacin zasu nemi gurfanar da jami'an gwamnatin Amurka. Koda kuma sun ki su amsa, zasu nemi a biyasu diya.