Wannan al'amarin da ya fi addabar zirga-zirgar jiragen sama a cikin Najeriya, ya fara shafar wasu jiragen masu tafiya kasashen waje, wadanda ala tilas sai sun tafi Kano ko kuma wata makwabciyar kasa kafin su samu man da zasu iya kammala tafiyarsu da shi.
Wakilin sashen Hausa, Ladan Ibrahim Ayawa, ya zagaya filin jirgin saman kasa da kasa na Murtala Muhammed dake Ikeja a Lagos, inda ya taras da matafiya da yawa wadanda suka koka kan yadda suka shafe tsawon sa'o'i da dama jirginsu bai tashi ba, yayin da wasu ma daga baya aka bayyana musu cewa an soke tashin jiragen kwata-kwata domin babu mai.
Babban darektan kamfanin zirga-zirgar jiragen sama mafi girma a Najeriya, Arik Air, Kyaftin Ado Sanusi, yace sun fara samun wannan matsala ta karancin mai tun ranar litinin.Kyaftin Sanusi yace sun saba adana lita dubu 500 na man jirgin, amma kuma wannan mai ba ya wuce kwana biyu yake karewa.
Babban darektan na kamfanin Arik Air yace idan har gwamnatin Najeriya ba ta gaggauta samo mafita daga wannan matsala ba, harkokin zirga-zirgar jiragen sama na iya tsayawa cik a kasar.
Babu dai wani kamfanin safarar jiragen sama a najeriya da ya kara farashin jirgin a dalilin wannan karancin mai da aka fara fuskanta.
Ga cikakken rahoton Ladan Ibrahim Ayawa daga Lagos.