Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fashewar Boma Bomai Har Uku Jiya A Potiskum Da Biu


wani hari da aka kai garin Potiskum
wani hari da aka kai garin Potiskum

Da missalin karfe biyar na marecen jiya ne aka samu tashin wani bom, a wajen wani dakin cin abinci da ake kira Al-amir Restaurant, kusa da gidan mai na Texaco a garin Potiskum dake jihar Yobe.

Wannan tashin bom din yazone bayan kwana bakwai da mazauna garin Patiskum sukayi yinkurin kame wani matashi daya shigo da bom a jikinsa, wanda daga bisani ya fada wani gida kuma bom din ya tashi harma ya hallaka shi.

Ko a jiya da rana an samu tashin wasu tagwajen bom a mashigar garin Biu, wanda akace yayi sanadin rayukan mutane goma sha hudu, wannan tashin boma bomai na ‘yan kwanakin nan yazone a dai dai lokacin da hukumomin tsaron Najeriya ke ikirarin sun sami kutsawa cikin dajin Sambisa, harma sun kwato wasu garuruwa dake hannun ‘ya ‘yan kungiyar Boko Haram.

Wasu ‘yan garin Potiskum, sun shaidawa wakilin mu Haruna Dauda Biu, ta wayar tarho cewa shi maharin yajene gidan cin abinci inda ya sayi abinci harma yake hira da mutanen dake zaune a gidan abinci, ance maharin ya dade a gurin kafin ya tayar da bom din nasa, wanda ya janyo mutawar mutane uku ciki harda da shi maharin.

Mai dakin cin abincin ya shaidawa wakilin namu Haruna, cewa mutane biyun da suka rasa rayukansu dalili tashin wannan bom din ‘ya ‘yan sane, kuma shi baya gari alokacin da wannan abun ya faru.

Shugaban karamar hukumar Biu, dake kudancin Borno, Alhaji Umar Kadafur ya tabbatar da cewa mutune goma sha hudu ne suka rasa rayukansu sakamakon tashin bom boman da maharan sukayi, kuma ake kyautata tsammanin cewar suna kokarin kutsawa ne cikin gari.

Hankulan jama’a musammamma matasa ‘yan aikin sa kai da ake kira ‘yan kato da gora ya karkatane wajen bincikar ababen hawa, dakuma lura da irin bakin da ka iya shigowa garinsu don bankado irin wadannan mahara dake hallaka mutanen da basu jiba basu gani ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG