A jihar ce lokacin kaddamar da kemfen din neman goyon bayan al'ummar jihar shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya lissafa ayyukan da gwamnatinsa zata aiwatar idan an zabeshi.
Abubuwan da zai yi sun hada da taimakawa marasa galihu da gine-gine da inganta rayuwar al'umma.
Yayinda wasu suka dauki kalamun Okpoko Atuahi da mahimmanci na cewar sai dan takara ya auri yar jiharsu kafin ya ci zabe, wasu kuma tur suka yi da kalamun.
Baba Gausu wani tsohon jamai'in tattaro jama'a na jihar ta Buni Afo a karkashin jami'iyyarsu ta NDC ya tabbatar da batun shi Mr. Atuahi. Yace tsohon shugaban kasar matarsa daga jihar ta ito. Wannan shugaban na yanzu matarsa daga jihar ta fito. Yace jihar ce kadai ta samu matan shugaba har biyu.
Jihar tana da tarihi na yanke hukumcin karshe kafin jam'iyya tayi mulki. Kawo yanzu ta jefawa shugabanni kusan ukku da suka yi mulki a kasar. Baba Gausu yace idan mutanen jihar suka ga kokarin dan takara suna mara masa baya. Idan an lura da ayyukan da shi shugaban kasan na yanzu yayi babu makawa zai sake lashe zabe, inji Baba Gausu.
Ga rahoton Baba Makeri Yakubu da karin bayani.