Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A jihar Neja jama'a sun goyi bayan cire tallafin man fetur


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari
Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

A yayinda kungiyar kwadagon Najeriya ke shirin tsunduma cikin yajin aikin gama gari al'ummar kasar na cigaba da bayyana ra'ayoyinsu akan dambarwar dake tsakanin gwamnati da kungyar kwadagon

Wasu al'ummar jihar Neja da suka zanta da Muryar Amurka sun yi watsi da barazanar da kungiyar kwadago ta yiwa gwamnatin kasar akan cire tallafin man fetur.

Sun nuna cewa suna tare da gwamnatin Muhammad Buhari kuma sun goyi bayan cire tallafin man duk kuwa da karin farashin litar mai din daga nera 86 zuwa 145.

Wani yace maganar yajin aiki da kungiyar kwadago tace zata yi idan domin talaka ne to a wannan karon talaka ya yafe. Su talakokin Najeriya gaba daya Allah ya ba iko suka zabi Shugaba Muhammada Buhari saboda haka basu goyi bayan yajin aiki da 'yan kwadago suke shirin yi ba.

Wani yace lokacin wancan mulki da aka so a cire tallafin shi ma ya goyi bayan kungiyar kwaqdago na cewa kada a cire. Yace a wancan lokacin koda an cire tallafin wadanda suke mulki ne zasu wawure kudin. Amma yanzu da Allah ya ba kasar shugaban da bashi da kwadayi zai yi anfani da kudin domin anfanin jama'a ne.

Amma sabon shugaban PDP na jihar Neja Barrister Tank Beji ya yi waiwaye ne akan lamarin. Yace lokacin da gwamnatinsu ta yi kokarin cire tallafin mai aka yi masu ca tare da cewa kasar zata rushe. To yau an cire tallafin kuma an yi kari yana son ya ga abun da 'yan Najeriya zasu yi.

Shi kuma kwamishanan labarai na jihar Mr. Jonathan Batsa yace ya yi imani Shugaba Muhammad Buhari ba zai cuci 'yan Najeriya ba. Ya dauki alkawari zai yi aiki tsakaninshi da Allah. Ya kira jama'a da su yi hakuri tare da yiwa shugaban addu'a.

A yanzu dai gobe ne wa'adin da kungiyar kwadagon ta ba gwamnati zai cika. Sai a sa ido a gani.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG