Shuwagabannin Kugiyar Izala ta kasa a Najeriya sun kawo ziyara kasar Amurka, inda suka yada zango a sashen Hausa na Muryar Amurka. Mun fara da tambayar Sheik Bala Abdullahi Lau, makasudin wannan ziyarar tasu.
Inda yace sun kawo wannan ziyarar ne bisa gayyatar da kungiyoyin musulunci suka yi musu, don yada da'awa da kuma ganin yadda addinin Islama ke kara samun karbuwa a idon duniya.
Yayi bayani da cewa sun ganema idon su irin nasarar da addinin ke samu a kasar, da kuma ganin yadda ake gudanar da taimakawa musulmai mazauna da 'yan kasar.
Kungiyar Izala ta dau alwashin taimakawa, da kuma ganin ta bada gudunmawa don ganin addinin ya samu karbuwa, da kuma kokarin yada koyarwar addinin Islama. Kamar yadda sauran duniya ke kallon addinin a matsayin addinin da bai son zaman lafiya.
Sheik Bala Lau, ya kara da cewa, addinin Islama addini ne da yake koyar da zaman lafiya da kaunar juna, ba wa mabiya addinin ba kawai harma da mabiya wasu addinai.
Facebook Forum