Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Arewa Sai A Hankali Sabanin Yadda Ake Yabawa Mawaka A Kudu


Said Young Arab.
Said Young Arab.

A matsayin mu na matasan mawaka masu tasowa mu kan samu kushewa daga wajen al'umma don kawai basa son abinda muke yi har wasu lokuta akan yi mana kallon bamu iya ba, daga cikin matsalolin da ke dakushe mawaka masu tasowa inji mawaki Said Young Arab.

Matashin ya kara da cewa sabanin yadda ake yi wa mawaka a kudu in da akasarin lokuta idan suna waka a wajen taro akan yaba ga mawaka ta hanyar basu kudade da kuma yi musu tafi ko karfafa musu gwiwa, hakan na daya daga cikin dalilan da suka sa mawaka a wancan wuraren ke samun cigaba a harkar wakarsu

Young Arab, ya ce sha’awa ce ta sa ya tsunduma ga harkar waka domin a cewarsa ta hanyar waka yana isar da sakonin zaman lafiya , mutunta juna da kuma hadin kai

Ya ce, a yanzu dai babban burinsa shine yayi fice a sanshi sannan ya samu damar mayar da wasu wakokinsa a faifan bidiyo , domin wakokinsa su sami fadada a kasa baki daya

Ko da yake y ace yana wakar hip-hop da rap wato gambara sannan da wakokin nanaye.

please wait

No media source currently available

0:00 0:07:43 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG