<!-- IMAGE -->
Shugabar kasar Liberiya ta hada manyan jami’an Nijeriya da na Libya wuri guda a wani kokarin sassauto da tankiyar da ta shiga tsakaninsu a bayan da shugaban kasar Libya ya ba da shawarar a raba Nijeriya gida biyu a tsakanin manyan addinanta.
Jiya laraba a birnin Abuja Ellen Johnson-Sirleaf ta gana da wani wakilin Libya da kuma mai rikon mukamin shugaban Nijeriya, Goodluck Jonathan.
Wani kakakin Nijeriya ya ce makasudin wannan ganawa shi ne aza harsashin amana tsakanin kasashen biyu ta yadda zasu iya shawo kan kalamun da shugaban Libya, Muammar Gaddafi, yayi kwanakin baya. Kakakin yace sassan biyu zasu ci gaba da tattaunawa.
A cikin watan jiya na Maris Gaddafi ya harzuka Nijeriya a lokacin da ya ba da shawarar da a raba kasar biyu ta koma kasar Musulmi da ta Kirista don kawo karshen rikicin addini. Daga baya sai ya ba da shawarar cewa a raba kasar zuwa kasashe da yawa domin kowace kabila ta dauki nata.
Nijeriya ta hasala har ta janye jakadanta daga Tripoli, tana mai bayyana kalamun na Gaddafi a zaman marasa karbuwa, kuma wadanda ba su kamanci shugaban da ya ce yana hankoron hada kan Afirka ba. Shugaban majalisar dattijan Nijeriya, David Mark, ya bayyana Gaddafi a zaman mahaukaci saboda shawarar cewa a raba Nijeriya.