<!-- IMAGE -->
Shugaba Muammar Gaddafi na Libya ya bayar da shawarar a raba Nijeriya kasa-kasa tsakanin kabilunta kamar yadda aka yi ad tsohuwar kasar Yugoslaviya, domin kawo karshen tashin hankali a kasar da ta fi kowacce yawan jama'a a nahiyar Afirka.
Wannan furuci nasa na jiya litinin, ya biyo bayan shawarar da ya bayar a makon da ya shige cewa a raba Nijeriya tsakanin kasar Musulmi da ta Kirista domin a kawo karshen zub da jinin addini.
A bayan kalamin na sa na makon jiya, Nijeriya ta janye jakadanta daga kasar Libya, tana mai bayyana kalamun na Gaddafi a zaman "maras karbuwa", wanda kuma bai kamanci shugaban da ke kururuta hada kan Afirka ba.
A lokacin da yake mayar da martani a jiya litinin, Gaddafi ya sake nanata ra'ayinsa na a raba Nijeriya, amma a wannan karon ba kasa biyu ba, a raba ta zuwa kasashe da dama kwatankwacin kabilunta.
Ya kwatanta Nijeriya da tsohuwar Yugoslaviya, wadda ta kasu zuwa kasashe da dama a bayan rushewar tsohuwar Tarayyar Soviet.
Gaddafi ya ce duk wani matakin da za a dauka na raba kasar da dukiyarta, ya kamata a yi ta hanyar tattaunawa da cimma yarjejeniya ba wai ta hanyar zub da jini ba.