Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mecece Murar Tsuntsaye?


Murar tsuntsaye (Avian Influenza) cuta ce wadda wasu kwayoyin halitta (Viruses) na mura suke haddasawa, akasari a jikin tsuntsaye, koda yake akwai lokutan da aka samu kwayoyin cutar a jikin aladu. Wadannan kwayoyin halittar cuta tun asali ma ana samunsu a jikin tsuntsaye.

Tsuntsaye na daji su na dauke da kwayoyin halittar cutar a cikin hanjinsu, kuma akasarin lokuta ba su yi musu komai. Amma kuma cutar murar tsuntsaye tana da saurin yaduwa a tsakanin tsuntsaye, kuma zata iya kama tsuntsaye da ake kiwo a gida, kamar kaji, agwagi da talo-talo, har ma ta kashe su.

Kwayar halittar cutar murar tsuntsaye tana janyo launin cutar biyu a jikin tsuntsaye na gida: mai tsanani da maras tsanani.

Gano cutar maras tsanani tana da wuya a saboda ba ta da alamu da yawa. Alamunta sun hada da mikewar gashi ko raguwar yawan kwan da tsuntsuwar ke yi.

Launin cutar mai tsanani yana da saurin ganowa. Yana yaduwa da sauri a cikin garken tsuntsaye, yana janyo cututtuka dake shafar sassa da yawa a cikin tsuntsaye, kuma kusan dukkan tsuntsayen da suka kamu da ita su na mutuwa, akasari cikin kwanaki biyu kadai.

XS
SM
MD
LG