Ana karkashe kaji da agwagi da sauran tsuntsaye danginsu yau litinin a Jamhuriyar Nijar, a ci gaba da yunkurin dakile yaduwar kwayoyin cutar murar tsuntsaye.
Wakilin Muryar Amurka a Yamai, Issoufou Mamane, ya ce ana gudanar da wannan aiki ne a kauyuka guda arba'in da shida inda aka samu bullar wannan cuta.
Gwamnati ta biya diyya ga mutanen da ake kashe tsuntsayen nasu.
Yayin da wannan yake faruwa ne kuma, jami'an Majalisar Dinkin Duniya, MDD, suka ce har yanzu murar tsuntsaye tana yin barazana mummuna duk da kokarin dakile yaduwarta.
Babban jami'in yaki da murar tsuntsaye na MDD, David Nabarro, ya ce an samu ci gaba a wasu wuraren. Amma kuma ya ce ganin an tare ci gaba da yaduwar cutar a wasu kasashe, bai kamata duniya ta yi sake a yunkurin da take yi na dakile yaduwar cutar ba.
(Domin jin cikakken rahoton kashe kaji a Nijar sai a matsa rubutun dake saman wannan labari a saurari rahoton Issoufou Mamane)