Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hamas Ta Mika Wa Isra'ila Gawarwakin Yahudawa Da Suka Mutu A Hannunta


Gawarwakin Yahudawa 4 da ake garkuwa da su a Gaza sun koma Isra’ila a yau Alhamis a musayar fursunoni ta baya-bayan nan karkashin yarjejeniyar tsagaita wutar da ke tsakanin Isra’ilar da kungiyar gwagwarmayar falasdinawa ta Hamas.

Daruruwan mutane ne suka taro a yankin Khan Yunis da ke kudancin birnin Gaza inda Hamas ta mika bakaken akwatunan gawa 4 ga kungiyar ba da agaji ta Red Cross, wacce ta yi safararsu cikin jerin gwanon motoci domin mikasu ga rundunar sojin Isra’ila.

Wata tawagar jerin gwano ta Isra’ila ta ratsa ta yankunan da mutane suka taru a gefen hanya rike da tutocin Isra’ila, sannan gawarwakin sun iso sa’o’i da dama daga bisani zuwa cibiyar binciken kwakwaf a fannin likitanci da ke birnin Tel Aviv domin tantance bayanan gawawwakin.

.
.

Mutanen da aka saki a yau Alhamis sun hada da mutum mafi kankantar shekaru cikin wadanda ake garkuwa dasu, jariri Kfir Bibas, wanda ke da watanni 9 lokacin da aka yi garkuwa da shi, sai dan uwansa mai shekaru 4, Ariel Bibas da kuma mahaifiyarsu, Shiri Bibas.

Dandalin Mu Tattauna

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG