Mubarak Bala mai shekaru 40 an maka shi a kotu ne sakamakon samun sa da laifukan sukar addini da wasu abubuwa da ya wallafa a shafin Facebook a shekarar 2020.
Kotu ta saki Mubarak Bala bayan da ya shafe shekaru hudu a gidan yari sakamakon kama shi da laifin batanci da sukar addini.
A ranar Laraba, dan majalisar dokokin Amurka, Mr. Jamie Raskin ya fitar da wata wasika, inda a cikin ta ya yi tsokaci akan shekaru biyar da Mubarak yayi a tsare, yana mai taya shi murnar shakar iskar ‘yanci.
Mr. Jamie Raskin yana cikin jerin hukumomi da kungiyoyin kasa da kasa na kare ‘yancin bil adama da ya bibiyi yadda aka gurfanar da Mubarak Bala a kotunan Kano da Abuja.
Bayan nazarin kunshin wasikar, wakilin muryar Amurka ya zanta da Mubarak Bala din inda yace, yana yiwa Mr. Jamie Raskin godiya sosai akan irin gudunmarwa da ya bashi.
Saurari tattaunawar cikin sauti:
Dandalin Mu Tattauna