Bankin duniya ya yi hasashen za’a samu matsaikaciyar bunkasar ta kaso 3.6 a tattalin arzikin Najeriya a tsakanin shekarun 2025 da 2026 sakamakon sauye-sauyen da gwamnatin tarayyar kasar ke gudanarwa.
Bankin ya bayyana hakan ne a cikin rahotonsa, na hasashen tattalin arzikin duniya na bana, da aka wallafa a jiya Alhamis.
Rahoton ya kara da cewa sauye-sauyen baya-bayan nan da gwamnatin Najeriyar ke aiwatarwa sun taimaka wajen bunkasa kwarin gwiwar yin kasuwanci.
Fitattu a cikin sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Najeriyar ke aiwatarwa sune janye tallafin man fetur da kuma kudirorin gyaran dokar harajin da suka janyo cece-kuce.
A cewar bankin duniyar “yawan arzikin da Najeriya ke samarwa, GDP, ya karu da kimanin kaso 3.3 cikin 100 a 2024, inda galibi hada-hadar bangaren ayyuka ne ya samar da shi, musamman bangarorin hada-hadar kudi da harkokin sadarwa.
“Ana hasashen bunkasar arzikin Najeriyar ta kara fadada zuwa kimanin kaso 3.6 cikin 100 tsakanin shekarun 2025 zuwa 2026. Sakamakon manufar takaita hada-hadar kudi ta 2024, ana hasashen raguwar hauhawar farashi sannu a hankali, inda za ta tallafawa bunkasar bangaren ayyuka, wanda ya kasance babban jigo na samun bunkasar arzikin.”
Dandalin Mu Tattauna