Wannan makon shirin ya kawo muku tattaunawar da Muhammad Bashir Ladan ya daga jagoranta a Yaounde babban birnin kasar Kamaru kashi na 6 kuma na karshe. Ya hada Matasa da manyan 'yan siyasa mahawara kan Mulkin dimokradiya a kasar Kamaru. Kasar da ta kasance cikin jerin kasashen da shugabanin su suka fi dadewa a mulki a Nahiyar Afirka baki daya. Shugaba Paul Biya ya yi shekaru 42 da yana mulki a kasar ta Kamaru. Matasan sun koka cewa ba ayi da su, ga rashin aikin yi, sannan manyan 'yan siyasar kuma, sun koka kan matsalar cin hanci da rashawa da suka ce ta dabaibaye kasar. Sun kuma bada shawara a yi wa kundin tsarin mulki da dokar zaben kasar garambawul, sannan sun nemi a bi dokar kasa idan ana so mulkin dimokradiya ya zama abin alfahari a Kasar.
Domin sauraron shirin tare da Medina Dauda, a latsa nan:
Dandalin Mu Tattauna