WASHINGTON, DC. —
Wannan makon, shirin ya dora ne akan tattaunawa da bbabban jami’in kula da ayyuka a hukumar kiyaye hadura reshen yankin arewa maso yammacin kasar Ghana, Mohammed Hashim Sidi Madani, a kan matakan da hukumar take dauka yayin da ake tinkarar watan Kresmeti da kuma babban zaben kasar da za ayi a ranar 7 ga watan Disamba, lokutan da ake yawan samun hatsira a kasar ta Ghana.
A makon da ya gabata bakon namu yana cikin bayani akan irin tarukan wayar da kan da suke shiryawa direbobi a tashoshin su.
A latsa nan don a saurari sautin shirin tare da Baba Y. Makeri:
Dandalin Mu Tattauna