A wani Mataki na kokarin shawo kan matsalar samun Yawaitar Hadurran jiragen ruwan kwale kwale a Nigeria Gwamnatin jihar Nejan Nigeriar ta kaddamar da Rabon jiragen ruwa na zamani a jihar,
Wannan dai a iya cewa shine karon farko da Gwamnatin tsakiya ta Dauki irin wannan Mataki da masana harkar sufutin ruwa sukace zai taimaka wajan samun nasarar kawar da tsoffin jiragen ruwa na katako da ake amfani dash tun kaka da kakanni,
Bayan mika jiragen ruwan na zamani guda biyar a garin wuya dake gabar kogin Neja Mataimaki na musannan akan kafofin sadarwa na zamani Alh. Abdulbaki Ebbo yace kokarin Gwamnatin jihar Nejan ne taga an samu Nasarar tsabtace harakar sufurin ruwa tare da kawar da duk wasu matsaloli dake haddasa Asarar rayukkan jama,a a cikin kogunan ruwa.
Yace Gwamnatin jihar Neja ta mika jiragen ruwa na zamani guda biyar masu daukar mugane Hamsin Hamsin dake zaune a gabar kogunan ruwa Domin kuwa wannan wani bangare ne na kokarin rage Yawaitar samun Hadurran jiragen ruwan kwale kwalen dake haddasa tabka Asarar rayukkan jama, a jihar,
Alh. Abdulbaki Ebbo yace tunda yanzu an samu wannan tallafi yana fatan masu amfani da jiragen ruwan zasu kiyaye,
Yace ina baiwa direbobin jiragen shawara da su tabbatar sumbi Dokokin hukumar kula da Dokokin safarar jiragen ruwa,
Tini dai masu aikin safarar jiragen ruwan suka nuna farin cikinsu akan samun wannan tallafi na Gwamnatin Shugaban kungiyar Direbobin jiragen ruwan a jihar Neja Hon. Attahiru Bawa Isa yace Lamarin yayi matukar Burgesu Domin hakan yanzu ya nuna cewa Gwamnatin ta fara sanin Muhimmamcin rayuwar Mutanen Bakin Ruwa,,
Shugaban na masu tuka jiragen ruwan Hon. Attahiru Bawa Isa yace suna kokarin fadakar da direbobin jiragen akan illar yin lodi fiye da kima da kuma tafiya cikin Dare..
Ko cikin Watan da ya gabata na satumba sama da mutabe 150 ne suka mutu Bayan da jirgin ruwansu ya kife akan hanyarsu ta zuwa wani taro na Maulidi a yankin mokwa ta jihar Nejan.
A saurari sautin shirin tare da Baba Y. Makeri:
Dandalin Mu Tattauna