Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Al’ummar Jihar Ondo Sun Kammala Kada Kuri'a A Mafi Yawan Rumfunan Zabe


Ma'aikatan Hukumar Zaben Najeriya wato INEC
Ma'aikatan Hukumar Zaben Najeriya wato INEC

A yau Asabar, 16 ga watan Nuwamba, 2024 ne al'ummar jihar Ondo za su zabi sabon gwamnan da zai jagorance su.

Gabanin zaben, hukumar zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta tantace jam’iyyun siyasa 18 da zasu fafata a zaben. Za a kada kuri'a a rumfunan zabe 3,933 na kananan hukumomin 18 dake jihar.

Mutane 2,053,061 ne suka yi rajistar zabe a jihar. Hukumar INEC ta ce za ta tura na'urar tantance masu kada kuri’a (BVAS) da bututun bayanai na (IReV) don gujewa tafka magudi.

A ranar Juma’a ne alkalan zaben suka fara rabon muhimman kayayyaki ga kananan hukumomin inda suka ce a shirye suke domin gudanar da zaben.

An baza ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro domin tabbatar da tsaro a jihar.

Gwamna mai ci Lucky Aiyedatiwa wanda ya gaji marigayi Gwamna Rotimi Akeredolu bayan rasuwar sa a karshen shekarar da ta gabata yana takara a zaben.

Sai kuma Babban abokin takarar sa Ajayi Agboola na jam’iyyar PDP, da kuma sauran ‘yan takara.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG