Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba A Samu Fitowar Jama’a Ba A Zaben Kananan Hukumomi A Jihar Kano


Masu kada kuri'a
Masu kada kuri'a

Zaben kananan hukumomi da aka yi a ranar sabar a jihar Kano ya gamu da kalubalen rashin fitowar jama’a rumfunan yayin da jami’an tsaro musamman ‘yan sanda basu fito aikin bada tsaro ba kamar yadda aka saba gani a lokuttan kada kuri’a.

Ba a ga fitowar jama’a ba a galibin mazabu da rumfunan zabe a sassan jihar ta Kano, yayin da wasu wuraren babu labarin kai kayayyakin zabe, kuma kalilan ne daga cikin cibiyoyin da suka samu kayayyakin zaben aka kammala zaben da karfe goma zuwa sha daya na rana.

Suma dai jami’an tsaro, musamman ‘yan sanda sun kauracewa wuraren kada kuri’a domin bada tsaro, kuma ta yuwu saboda hukuncin babbar kotun tarayya ta Kano ne, da ya haramta musu halartar cibiyoyin zaben.

Wasu kadan daga cikin mutanen da suka je rumfunan zaben domin kada kuri’a, sunce sunyi amfani da dokar kasa da ta basu damar kada kuri’ar su ga wanda suke so, kuma ‘yan kwamitin tsaro da suka kunshi jami’an tsaron sa kai dana Karota sun bada kariyar tsaro a rumfunan zabe.

Ana ganin baya ga dambarwar shari’a data dabaibaye sha’anin zaben da yanke kauna ga yin adalci ko sahihanci akan harkar zaben kananan hukumomi a Najeriya, matsin rayuwa a kasa na daga cikin dalilan da suka sa dinbin mutanen jihar Kano suka kauracewa wannan zaben na 26 ga watan na Oktoba.

Manyan jam’iyyun hamayya, PDP da APC ba su shiga zaben ba, amma a cewar shugaban hukumar zaben ta Kano Farfesa Sani Lawan Malumfashi, 6 daga cikin kananan jam’iyyu a Najeriya da suka hada da AA, AAC ACCORD, ADC APM da kuma jam’iyyar NNPP mai gwamnati a jihar Kano, sun shiga zaben.

Kano dai na cikin rukunin karshe na jihohin dake fafutikar samar da zababbun shugabanni a kananan hukumomi da nufin cika umarnin kotun kolin Najeriya, wadda ya haramta nada kantomomi da gwamnoni ke yi su tafiyar da mulkin kananan hukumomi a Najeriya.

Dandalin Mu Tattauna

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG