Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Karbi Alluran Rigakafin Malaria 846, 000 Daga GAVI


Wata mai jinya rike da allurar riga-kafin Astrazeneca a Najeriya
Wata mai jinya rike da allurar riga-kafin Astrazeneca a Najeriya

Za a fara raba alluran rigakafin ga jihohin da suka fi fama da annobar, musamman ma Kebbi da Bayelsa kuma hakan zai zama kari ne akan sauran magungunan maleriyar da ake dasu.

Najeriya ta karbi rukunin farko na alluran rigakafin zazzabin ciwon sauro samfurin R21 guda 846, 000, daga kawancen kasa da kasa akan samar da alluran rigakafi (GAVI).

Kaddamar da alluran rigakafin da aka yi a hukumance a yau Alhamis ya samu halarcin jami’ai daga ma’aikatar lafiya ta tarayya da hukumar kula da kiwon lafiya a matakin farko (NPHCDA) da hukumomin bada agaji.

Ministan Lafiyar Najeriya, Farfesa Ali Pate, ya bayyana isowar alluran rigakafin a matsayin wata muhimmiyar hobbasa daga bangaren gwamnati a kokarin da take yi na kawar da annobar maleriya daga kasar.

Ya kara da cewa za’a fara raba alluran rigakafin ga jihohin da suka fi fama da annobar, musamman ma Kebbi da Bayelsa kuma hakan zai zama kari ne akan sauran magungunan maleriyar da ake dasu.

Farfesa Pate ya kuma kawar da damuwar da ake da ita game da ingancin alluran rigakafin, inda yace an tabbatar da inganci da rashin hatsarin maganin na maleriya.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG