Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutum 9 Na Mutuwa Kowace Sa'a Sakamakon Maleriya A Najeriya - Minista


MALARIA MOSQUITO
MALARIA MOSQUITO

Rahoton hukumar lafiya ta duniya ya nuna cewa Najeriya kadai ce take da kashi 27 cikin dari na dukan cutar maleriya a duniya, haka kuma kasar ce ke da kashi 23 na adadin mutanen da cutar ke kashewa a fadin duniya.

Kididdiga ta bayyana cewa cutar zazzabin cizon sauro wato maleriya, tana haddasa mutuwar mutane 9 a kowace sa’a a Najeriya.

Ministan Lafiya na Najeriyar Osagie Ehanire ne ya bayyana haka, sa’adda wata tawagar ma’aikatarsa tare da ta hukumar kula da lafiyar iyali wato ‘Soceity for Family Health’ suka kai ziyarar ba girma ga mataimakiyar gwamnan jihar Ogun, a wani gangamin hadin gwiwa na yaki da cutar maleriya.

Ministan ya bayyana damuwa da yadda cutar ta maleriya take kara habaka, tare da haifar da lahani ga rayuwar ‘yan Najeriya.

Osagie Ehanire
Osagie Ehanire

Ya ce a cikin kowadanne mutane 4 da ke da cutar maleriya a duk fadin duniya, daya yana a Najeriya.

Rahoton hukumar lafiya ta duniya kuma ya nuna cewa Najeriya kadai ce take da kashi 27 na dukan cutar maleriya a duniya, haka kuma kasar ce ke da kashi 23 na adadin mutanen da cutar ke kashewa a fadin duniya.

Akan haka Ministan ya ce ya zama wajibi a dauki kwararan matakai na yaki da cutar, domin dakile munin da take haifarwa na kisan jama’a a fadin kasar.

ABUJA: Taron kasashen dake fama da cutar malaria
ABUJA: Taron kasashen dake fama da cutar malaria

Ya ce yanzu haka ma’aikatar lafiya ta tarayya, tare da hadin gwiwar hukumar ta kula da lafiyar iyali da kuma shirin yaki da maleriya na kasa, sun shirya rarraba gidajen sauro masu magani har miliyan 3.7 da za’a rarrabawa iyalai a dukkan kananan hukumomi 20 na jihar ta Ogun.

XS
SM
MD
LG