Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma’aikatan NAFDAC Sun Tsunduma Yajin Aiki


NAFDAC
NAFDAC

Sanarwar dake dauke da sa hannun sakataren kungiyar ta SSASCGOC kwamred Ejor Micheal ya umarci ma’aikata su tsunduma cikin yajin aikin tun daga yau Litinin.

Reshen hukumar tabbatar da inganci abinci da magunguna ta Najeriya (NAFDAC) na kungiyar manyan ma’aikatan hukumomi da kamfanonin gwamnati (SSASCGOC), wanda wani reshe ne na kungiyar kwadago ta tuc, ya tsunduma cikin yajin aikin sai baba ta gani saboda gazawar hukumar wajen warware matsalolin dake da nasaba da walwalar mambobinsa.

Sanarwar dake dauke da sa hannun sakataren kungiyar ta SSASCGOC kwamred Ejor Micheal ya umarci ma’aikata su tsunduma cikin yajin aikin tun daga yau Litinin.

“Bayan tattaunawa a hankali, kungiyar ta yanke shawarar tsunduma yajin aikin sai baba ta gani a dukkanin ofisoshin NAFDAC dake fadin Najeriya, tun daga yau Litinin, 7 ga watan Oktoban da muke ciki.” A cewar sanarwar.

A cewar sanarwar bayan taron da aka fitar a ranar 4 ga watan Oktoban da muke ciki, ma’aikatan da al’amarin ya shafa sun ce daukar matakin ya zama wajibi bayan dimbin zaman da suka yi da hukumar gudanarwarsu akan batutuwan da suka shafe karin girma da albashi da walwalarsu inda har yanzu kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG