Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwale-Kwale Ya Kife Da Mutum 300 A Neja


Hatsarin kwale-kwale a jihar Kebbi
Hatsarin kwale-kwale a jihar Kebbi

A cewar sanarwar da sakataren yada labaran karamar hukumar Mokwa, Abubakar Dakani ya fitar, kwale-kwalen na dauke ne da fiye fasinjoji 300 lokacin da ya kife a kogin Gbajibo da ya yi kwaurin suna a karamar hukumar ta jihar Neja.

An tsamo akalla gawawwaki 60 daga wani hatsarin kwale-kwale daya afku a jihar Neja.

A cewar sanarwar da sakataren yada labaran karamar hukumar Mokwa, Abubakar Dakani ya fitar, kwale-kwalen na dauke ne da fiye fasinjoji 300 lokacin da ya kife a kogin Gbajibo da ya yi kwaurin suna a karamar hukumar ta jihar neja da yammacin jiya Litinin.

A cewar Dakani kwale-kwalen na kan hanyarsa ne daga garin Mundi zuwa Gbajibo domin halartar bikin Maulidi sa’ilin da iftila’in ya afku.

Sanarwar ta ruwaito shugaban karamar hukumar Abdullahi Muregi ya na tabbatar da tsamo akalla gawawwaki 60, inda aka samu mutane 10 da ransu.

Ta kara da cewa ana ci gaba da aikin ceto da hadin gwiwar hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Neja domin gano sauran mutane da suka bace.

A nashi sanarwar, kakakin hukumar agajin gaggawa ta jihar, Abdullahi Baba Arah, ya ce an ceto mutum fiye da 150 da ransu.

A watan Satumbar 2023, irin wannan kwale-kwale dauke da fiye da fasinjoji 50 ya kife tare da hallaka mutane 24 wadanda ke kan hanyarsu ta zuwa gona domin girbin amfaninsu.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG