Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

DOMIN IYALI: Nazari Kan Tasirin Dokar Kare 'Yancin Kananan Yara a Najeriya-Kashi Na Biyu, Agusta, 08, 2024


Alheri Grace Abdu
Alheri Grace Abdu

A ci gaba da nazarin tasiri ko akasin haka na dokar kare hakkin kananan yara bayan sama da shekaru 20 da gwamnatin tarayyar Najeriya ta kafa ta, batun da ya dauki hankalin babban taron kungiyar lauyoyi mata na kasa da jihar Kano ta karbi bakunci. Yau bakin da Shirin Domin Iyali ya gayyata sun bayyana abinda ya hana rungumar dokar.

Bakin da shirin ya gayyata sun hada daBarista Bilkisu Ibrahim Sulaiman shugabar kungiyar lauyoyi mata reshen jihar Kano, da Barrista Ibrahim Chedi tsohon ma’ajin kungiyar lauyoyi na kasa reshen jihar Kano, da kuma magidanci da ke wakiltar iyaye a wannan zaman Malam Aminu Muhammad Adam .

Saurari cikakken shirin:

DOMIN IYALI: Nazari Kan Tasirin Dokar Kare 'Yancin Kananan Yara a Najeriya-Kashi Na Biyu
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:35 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG