An sami rarrabuwar kai tsakanin mabiya addinin kirista na ikilisiyar United Methodist Church, UMC, a Najeriya sakamakon matsayar da majalisar gudanarwar ikilisiyar ta cimma na amincewa da ayukan luwadi, madigo da auren jinsi.
Majalisar ta UMC ta yi wannan matsayar ne a babban taronta na bayan kowacce shekara hudu da ta gudanar a Amurka. To sai dai kuma da alama matsayar ba ta sami karbuwa ba a tsakanin mabiya ikilisiyar a Najeriya, wadanda suka gudanar da zanga-zangar lumana a wani taro da suka gudanar makon jiya a Bauchi da ke Arewacin Najeriya.
Wannan ya sa mabiya ikilisiyar suka kuma gudanar da wani taron a shelkwatar UMC din da ke Jalingo a jihar Taraba, inda suka yi matsayar ficewa daga ikilisiyar ta United Methodist Churh UMC, zuwa Global Methodist Church, GMC.
Bishop John wesley Yohanna shi ne Shugaban ikilisiyar da ya jagoranchi taron, ya kuma ce sun yanke shawarar sauya shekar ne saboda ba za su zauna a ikilisiyar da ta amince da luwadi, madigo da auren jinsi ba.
Bishop Yohanna ya ce “Littafin Bible ya hana, dokar kasarmu ta hana, kuma ya saba wa al’adunmu. Saboda haka mu za mu bi abin da Bible ya fada, kuma ba za mu yi abin da za mu janyo wa ‘ya’yanmu da al’ummarmu illa ba.”
To sai dai Rev Ande Emmanuel, daya daga cikin wasu kalilan da basu amince da sauya shekar ba, ya ce suna nan daram a cikin UMC, duk kuwa da cewa su ma ba su yarda da luwadi da madigo da auren jinsi ba.
Saurari cikakken rahoton Lado Salisu Garba:
Dandalin Mu Tattauna