Firayim Ministan Australiya ya wallafa a kan X cewa, "muna godiya da jagorancin ku da kuma ci gaba da shugabancin da Biden ya kawo. Alakar Australiya da Amurka ta yi karfi tare da hadin gwiwarmu ga bangaren dimokiradiyya, tsaro na kasa da kasa, wadatar tattalin arziki da bangaren sauyin yanayi domin magadanmu."
Firayim Ministan Biritaniya Sir Keir Starmer ya wallafa a kan X cewa yana mutunta Biden akan yanke shawarar janyewa daga takarar, kuma yana fatan yin aiki tare da shi kafin saukar sa.
Firayim Ministan Canada ya wallafa a kan X cewa, "Na san Shugaba Biden tsawon shekaru. Shi mutum ne mai karamci, kuma yana jagoranci saboda kaunarsa ga kasarsa. A matsayinsa na shugaban kasa, abokin tarayya ne ga al’ummar."
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya wallafa akan X cewa, ya yaba wa Biden kuma "ya sami nasarori da yawa ga kasarsa, da Turai, dama duniya baki daya."
Shima Shugaban Isra'ila ya nuna godiyarsa ga Biden saboda "tabbataccen goyon bayansa ga al'ummar Isra'ila" a tsawon shekaru da ya kwashe yana aiki.
Herzog ya wallafa cewar, "A matsayinsa na shugaban Amurka na farko da ya ziyarci Isra'ila a lokacin yaki, a matsayinsa na wanda ya samu lambar yabo, kuma a matsayinsa na abokin kawancen Yahudawa na hakika, alama ce ta alakar da ke tsakanin al'ummominmu."
Ita ma Kremlin ta fada a jiya Lahadi cewa, tana sa ido sosai kan abubuwan da ke faruwa a Amurka bayan da Biden ya yanke shawarar janyewa daga takara.
Kakakin Kremlin Dmitry Peskov ya shaidawa wata kafar yada labarai ta Rasha cewa, “saura watanni hudu a gudanar da zaben Amurka, kuma lokaci ne mai tsawo da abubuwa da yawa za su iya canzawa. akwai bukatar mu yi hakuri kuma mu sa ido sosai kan abin da ke faruwa. Muhimman abubuwa a gare mu shi ne aikin soji na musamman."
Shima Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya bayyana cewa, shawarar da Biden ya dauka na janyewa daga takara abu ne mai "tsaurin gaske".
Zelenskyy ya wallafa a shafin X cewa, "Za mu kasance ko yaushe masu godiya ga shugabancin Biden, da irin goyon bayan da ya bawa kasarmu a lokaci mai tattare da tarihi, ya taimaka mana wajen hana Putin mamaye kasarmu, kuma ya ci gaba da ba mu goyon baya a cikin wannan mummunan yakin. A halin da ake ciki a Ukraine da ma Turai baki daya, ba karamin kalubale bane, kuma muna fatan shugabancin Amurka zai ci gaba da hana Rasha yin nasara akan ta'addancinsu."
Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ba ta ce komi ba akan batun ta bangaren diflomasiya, da suka hada da Sakataren Harkokin Wajen Antony Blinken da takwarorinsa.
Blinken ya wallafa a kan shafin X cewa, ya yi aiki da Biden tsawon shekaru 22, kuma zai ci gaba da aiki da Biden a cikin watanni shida masu zuwa domin inganta shugabancin Amurka.
Dandalin Mu Tattauna