Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Al’ummar Iran Na Nuna Girmamawar Karshe Ga Gawar Shugaba Ra’isi Daya Mutu A Hatsarin Jirgin Shelkwafta


Iran
Iran

Dubban al’ummar Iran ne suka hallara a yau Talata domin alhinin mutuwar shugaban kasar Ebrahim Ra’isi tare da ‘yan tawagarsa 7 da suka hallaka a hadarin jirgin saman shelkwafta akan wani tsauni da hazo ya lullube a arewa maso gabashin kasar.

Masu alhinin dauke da tutocin Iran da hotunan shugaban kasar sun faro gangamin ne daga tsakiyar wani dandali dake birnin Tabriz na shiyar arewa maso yammacin kasar, inda Ra’isi yake nufin zuwa sa’ilin da jirgin saman da yake ciki yayi hatsari a Lahadin data gabata.

Masu alhinin sun yi tattaki a bayan babbar motar dake dauke da gawar Ra’isi da sauran hadimansa 7.

An daina jin duriyar jirgin saman shelkwaftan yayin da yake kan hanyarsa ta komawa Tabriz bayan da Shugaba Ra’isi ya kaddamar da aikin ginin madatsar ruwa ta hadin gwiwa dake kan kogin Aras, dake kan iyakar Iran da Arzebaijan, a wani kwarya-kwarya biki daya gudana tare da takwaransa Ilham Aliyev.

An kaddamar da wani gagarumin aikin ceto a Lahadin da ta gabata bayan da jiragen saman shelkwafta dake yiwa wanda Ra’isi ke ciki rakiya suka daina jin duriyarsa sakamakon rashin kyawun yanayi.

Sauran wadanda suka mutu tare da ra’isi sun hada ministan harkokin wajen kasar, hossein amir abdollahian, da jami’an yankin tabriz da kuma askarawan dake tsaron lafiyar shugaban kasar.

Shugaban Ma’aikatan Rundunar Sojin Iran, Muhammad Bagheri ya bada umarnin binciko musabbabin hatsarin jirgin saman a daidai lokacin Iraniywa a ilahirin manyan biranen kasar suka yi dafifi domin alhinin mutuwar ra’isi da ‘yan tawagarsa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG