Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin Da Sojin Najeriya Suka Kai Maboyar 'Yan Ta'adda A Zamfara Ya Hallaka Mayakansu Da Dama


Babban Hafsan Tsaron Najeriya Janar Christopher Gabwin Musa
Babban Hafsan Tsaron Najeriya Janar Christopher Gabwin Musa

WASHINGTON DC - Dakarun Sojin Najeriya da aka tura aikin wanzar da zaman lafiya a jihohin Katsina da Zamfara sun kaddamar da hare-hare a maboyar 'yan ta'ddar abinda yayi sanadiyar halaka wasu daga cikinsu.

A sanarwar data wallafa a shafinta na X a yau litinin, Rundunar Sojin Najeriya tace a samamen data kaddamar a jihar Zamfara a ranar 29 ga watan Maris din daya gabata, dakarunta sun kai hare-hare a maboyar kasurgumin dan bindigar nan Hassan 'Yantagwaye dake karamar hukumar Tsafe.

Ana zargin 'yantagwaye da yaransa da hannu a sace-sacen jama'a da ayyukan ta'addanci a wasu sassa na shiyar arewa maso yammacin Najeriya.

A yayin samamen, dakarun sojin sun yi galaba akan 'yan bindigar a wata zazzafar musayar wuta, inda suka hallaka 3 daga cikinsu tare da kwato dimbin makamai harma da lalata maboyarsu.

Har ila yau, a ranar 29 ga watan Maris din daya gabata, Rundunar Sojin Najeriya tace tayi nasarar kwace kulli 441 na wani abu da ake zargin tabar wiwi ce a kauyen molegede dake karamar hukumar odeda ta jihar ogun.

Bugu da kari, rundunar tace a ranar 30 ga watan Maris din daya gabata, dakarunta dake jihar Katsina sun yi musayar wuta da 'yan ta'adda a garuruwan Shawu Kuka da Shinda da Tafki da Gidan Surajo da Citakushi dake yankunan Kabai Ta 1 da ta 2 dukkaninsu A karamar hukumar Faskari.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG