'Yan sandan kasar Spain sun kama wasu mutane uku kan mutuwar wasu bakin haure biyar da aka tilasta musu su tsuduma cikin teku daga cikin wani jirgin ruwa mai gudu da gangan a watan Nuwamban da ya gabata, kusa da gabar tekun Atlantika da ke Cadiz a kudancin Spain.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ce an tsare maza biyu da mace daya a yankin Algeciras mai tazarar kilomita 70 kudu maso gabashin Cadiz. Ana zarginsu da tilastawa bakin hauren yin tsalle cikin teku yayin da su ke masu barazana da wuka duk da sanin cewa da yawan bakin haure ba su iya iyo ba.
Ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar ta ce ana kuma zargin mutanen ukun da kasancewa 'yan kungiyar masu aikata laifukan cin zarafin 'yan kasashen waje, ji wa mutane raunuka da kuma fasa kwauri.
Gwamnatin kasar ta ce adadin bakin hauren da suka isa kasar ta Spain cikin kwale-kwale a cikin watanni biyun farko na wannan shekara ya ninka sau hudu zuwa 13,485 daga daidai wannan lokacin na shekara guda da ta gabata, kamar yadda bayanan ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar suka nuna.
Dandalin Mu Tattauna