Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zanga-Zanga Akan Tsadar Rayuwa Ta Sabbaba Rufe Tituna A Birnin Minna


Mazauna birnin Minna da ke zanga-zanga Akan tsadar rayuwa
Mazauna birnin Minna da ke zanga-zanga Akan tsadar rayuwa

A  yau litinn, mazauna Minna, babban birnin jihar Neja sun gudanar da zanga-zanga game da tsadar rayuwa a Najeriya, inda suka toshe manyan titunan birnin.

An jiyo masu zanga-zangar da suka hada da mata da matasa suna rera wakokin gwagwarmaya, a yayin da jami’an tsaro ciki harda ‘yan sanda ke kallo.

A cewar masu zanga-zangar, hauhawar farashin kayan masarufi da rashin daukar kwakkwaran mataki daga bangaren gwamnati ya sanyasu datse manyan hanyoyi da nufin janyo hankalin gwamnatin ta sauraresu.

Mazauna birnin Minna da ke zanga-zanga Akan tsadar rayuwa
Mazauna birnin Minna da ke zanga-zanga Akan tsadar rayuwa

A jawabinsa ga masu zanga-zangar, Mataimakin Gwamnan Jihar Neja, Yakubu Garba, yace gwamnati tana sane da irin mawuyacin halin da al’umma ke ciki a halin yanzu.

Ya kara da cewar gwamnati na aiki tukura wajen ganin ta sassauta matsalar tsadar rayuwa da mawuyacin halin da janye tallafin man fetur ya haifar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG