Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Alhazan Najeriya Ta Kara Kudin Aikin Hajjin Bana


Saudi Arabia Hajj
Saudi Arabia Hajj

Hukumar alhazan Najeriya (NAHCON) ta ayyana farashin kujerar hajjin bana da ya doshi Naira miliyan 5.

Hukumar ta kara kudin aikin hajjin 2024 yayin da darajar Naira ke ci gaba da faduwa a kan dalar Amurka.

Tun da farko hukumar ta sanar da Naira miliyan 4,500,00 a matsayin kudin aikin hajjin 2024, amma yanzu kudin ya kama daga Naira miliyan 4,999,000 daga kudanci zuwa Naira miliyan 4,699,00 a arewa, yayin da a arewa maso gabas, Maiduguri da Yola mafi kusanci da Saudiyya ya ke Naira 4,679,000.

Sanarwa daga jami'ar labarun hukumar NAHCON, Fatima Sanda Usara, ta ce karin kan kudin ajiya tun farko Naira miliyan 4.500,000 ya karu ne don yadda dala ke ci gaba da cillawa sama.

Fatima ta ce karyewar darajar Naira ne ya sanya wannan karin, kamar yadda hakan yasa hukumar ta sake duba kudin.

Hukumar NAHCON ta kara da cewa don kokarin da ta yi na neman rangwame ga lamura da dama na hidimar alhazai da tikitin jirgi ya samar da sabon farashin wanda in ba don haka ba da kudin kujerar zai kai Naira miliyan 6,000,000.

Hukumar ta NAHCON ta bukaci wadanda suka biya kudin ajiya da su cika gabanin wa’adin ranar 25 ga watan Fabrairu da aka tsayar.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG