Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawa Ta Gayyaci Jami'an Tsaron Najeriya Kan Matsalar Tsaro


ABUJA: Shugaban Majalisar Dattawa yana yiwa 'yan jarida jawabi
ABUJA: Shugaban Majalisar Dattawa yana yiwa 'yan jarida jawabi

Majalisar Dattawa ta sake gayyatar daukacin jami'an tsaron kasar a mako mai zuwa domin tattaunawa tare da samar da mafita kan matsalar rashin tsaro da ta addabi kasar.

Matsalar rashin tsaron dai , wani babban batu ne da aka dade ana tattauna shi a zauren Majalisar inda 'yan Majalisar suka baiyaya damuwarsu kan yadda kashe kashe, 'yan fashi da makami , sace sacen mutane don karban kudin fansa, da duba yadda aka ma kashe wadanda aka biya kudin fansa kansu, da kuma kashe wasu shugabanin gargajiya biyu da sace daliban makaranta a jihar Ekiti da duk wani nau'i na laifuka a fadin kasar ciki har da babban birnin tarayya.

A hirar shi da Muryar Amurka, Sanata mai wakiltar Nasarawa ta Yamma Ahmed Aliyu ya bayanna cewa, tun kafin su tafi hutun karshen shekara ne suka amince da gayyato Shugabanin Hukumomin tsaron a bisa dalilan tsaro da ke kara tabarbarewa maimakon raguwa. Ya bayyana cewa, duk da yake an jima ana gayyato shugabanin hukumomin tsaron amma ba a ganin cigaba, a wannan karon, matakin da Majalisar za ta dauka zai banbanta, kuma za su baiyana wa yan kasa duk matakin da za a dauka domin shawo kan lamarin.

To sai dai kwararre a fanin tsaro Dokta Yahuza Ahmed Getso ya kushewa wannan yunkuri da Majalisar ta ce za ta yi yana mai cewa, gayyata da Majalisar ta ke yi wa Shugabanin hukumomin tsaron abinda Hausawa ke cewa "tabarmar kunya da hauka ake nade ta ne", domin babu wata alaka da bayanin da jami'an tsaron za su zo su bada da abinda ke faruwa a zahirance. Yahuzu ya ce majalisa ce ya kamata ta sa ido wajen ayyukan jami'an domin sun riga sun saki kudaden da ya kamata a yi aiki da su.

A nashi bayanin, mataimakin jami'in Mu'amala da baki na kungiyar Human Right Network Nura Muktar Tsanya ya nuna takaicin sa ne tare da ba shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu shawara cewa, duk jami'in da bai yi aikin sa yadda ya kamata ba, a cire shi a sa wani a madadinsa.

Jami'an tsaron da ake sa ran bayyanar su a gaban Majalisar sun hada ne da mai ba shugaban kasa shawara a harkar tsaro Nuhu Ribadu da sauran su.

Saurar cikakkeni rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:15 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG