AGADEZ, NIGER - Taken bukin na bana shi ne: "Malaman da muke bukata domin ilimin da muke so; Dole ne duniya ta tashi domin magance karancin malamai”
Bikin na bana na so ne duniya ta mayar da hankali kan yadda za’a magance matsalar raguwar malamai, a kuma samar da hanyoyin da za’a kara yawansu a ko yaushe, kuma bikin na bana yazo ne a Nijar a daidai lokacin da har yanzu ba’a biya wasu daga cikin malaman albashin su ba.
Malaman makarantu a Nijar na fama da fargaba ta rayuwarsu yayin da kuma matsin tattalin arziki ke jefa malamai da yawa cikin mawuyacin hali inda albashin da ake biyansu ke karewa a cikin sati guda.
Kungiyar malaman ta tabbatar da halin da malamai a Nijar suke ciki a wannan sashen da duniya ke cewa abin tausayawa ne.
Traore Hamidou shugaban gamayyar kungiyoyin malamai a jihar Agadas ta Jamhuriyar Nijar, ya ce manyan matsalolin da ake fuskanta a bangaren koyarwa shine karancin malamai na dindindin musanman a makarantun firamare da ake kallo a matsayin tushe na ginin ilimin bil’adam.
To saidai shugabannin ilimi sun yaba da irin kokarin da malamai ke yi da ma gudummawar da suke bayarwa wajen inganta ilimi.
Hukumar raya ilimi da kimiya da al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO, ta ce samar da kyakkyawan yanayin ilmi da kuma tsarin karatu mai kyau shi ake so ya zama burin al’ummar duniya.
To sai dai a kullum masu sharhi na aza laifin tabarbarewar ilimi kan hukumomi, su kuma hukumomin suna cewa suna iya kokarinsu domin inganta ilimi
Saurari açıkken rahoto daga Hamid Mahmud:
Dandalin Mu Tattauna