Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shekara Daya Bayan Mamayar Da Rasha Ta Yi wa Ukraine


Yadda kasashen duniya suke bikin tunawa da fara yakin Ukraine
Yadda kasashen duniya suke bikin tunawa da fara yakin Ukraine

Kasashe kawayen Ukraine a fadin duniya sun baje kolin muhimman wuraren tarihi, tare da shirya sabbin takunkumai, a wani taron baje kolin nuna goyon baya na bikin cika shekara daya da mamayar da Rasha ta yi wa kasar.

A Jamus, wacce ta kawar da tsarinta na kasuwanci da Rasha tare da tura makamai zuwa Ukraine, Shugaba Frank-Walter Steinmeier ya ce mamayar tamkar wani koma baya ne kan darasin yake-yaken duniya biyu.

Firayim Ministan Poland Mateusz Morawiecki ya tafi Kyiv, tare da Firayim Ministan Ukraine, inda suka shimfiɗa furanni a bangon tunawa da waɗanda suka mutu a tafarkin kare Ukraine.

Amurka ta yi bikin zagayowar ranar ne ta hanyar sanar da sabbin takunkumai kan Rasha da kawayenta, da sabbin matakan kayyade fitar da kayayyaki zuwa kasashen ketare da kuma haraji, tare da nufin kawo tarnaki ga yunkurin Moscow na kara shirin yaki.

Ita ma Biritaniya ta fitar da na ta sabbin takunkumai.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG