Yawan Jihohin Da Manyan Jam'iyu Su Ka Lashe
APC-12
PDP-12
LP-12
NNPP-1
Shugabanni Yammacin Afirka Sun Bukaci INEC Ta Kiyaye Dokar Zabe
Shugabanni a yankin yammacin Afirka sun bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da ta bi tanade-tanaden dokar zabe ta 2022 dangane da tattara sakamakon zaben shugaban kasa da na 'yan Majalisar dokokin kasar da aka gudanar a ranar Asabar.
Wakilan kungiyar dattawan Afrika ta Yamma (WAEF) ne suka yi wannan kiran a Najeriya, ciki har da tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan da tsohon shugaban Ghana John Mahama, a wata sanarwa da suka fitar jiya Talata a Abuja.
Shugabannin sun kuma yi kira da a kwantar da hankula a kasar, tare da yin kira ga INEC da ta magance matsalolin da masu ruwa da tsaki daban-daban suka gabatar dangane da harkokin zabe.
Sakamakon Zaben Shugaban Kasa
APC-8,794,726
PDP-6,984,520
LP-6,101,533
NNPP-1,496,687
Tinubu Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa
Dan takarar jam’iyar APC, Bola Tinubu ya lashe zaben shugaban kasa bayan ya sami kashi 36% na kuri’un da aka kada a zaben shugaban kasa da aka gudanar ranar asabar, yayinda dan takarar jam’iyar PDP Atiku Abubakar ya zo na biyu da kashi 30% dan takarar Jam'iyar Labour Peter Obi kuma ya zo na uku da kashi.26%.
Tinubu ya doke sauran ‘yan takara goma sha takwas da kuri’u APC-8,794,726, yayinda dan takarar jam’iyar PDP Atiku Abubakar ya sami kuri’u 6,984,520, Peter Obi na jam’iyar Labour ya sami kuri’u 6,101,533, yayinda dan takarar jam’iyar NNPP-Rabi’u Musa Kwankwaso 1,496,687.