Sakamakon Zaben Jihar Akwa Ibom
APC-160,620
PDP-214,012
LP-132,69
Yawan Jihohin Da Manyan Jam'iyu Suka Lashe
Bayan sanar da sakamakon zaben jihohi 28, da kuma na babban birnin tarayya Abuja, jam'iyar PDP tana gaba da yawan jiho, sai jam'iyar APC na biyu, sai kuma jam'iyar Labour, kana jam'iyar NNPP a matsayin karshe.
Ga adadin jihohin da jam'iyun suka lashe:
APC-9
PDP-12
LP- 6 + FCT
NNPP-1
NNPP Ta Bi Sahun PDP, LP Wajen Neman A Soke Zaben Shugaban Kasa A Najeriya
- By Mahmud Lalo
Jam’iyyar NNPP ta bi sahun PDP da LP wajen yin kira da a soke zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da aka yi.
“Domin ceto mulkin dimokradiyya da kasarmu, wannan sakamakon zabe ba zai samu karbuwa a wajen ‘yan Najeriya da kawayen Najeriya ba. Saboda haka, muna kira da a yi hanzarin dakatar da sanar da sakamakon zaben a kuma soke zaben shugaban kasar a duk fadin kasar.” Shugaban jam’iyyar NNPP, Farfesa Rufa’i Alkali ya ce a wani taron manema labarai.
Sakamakon Zaben Jihar Ribas
APC-130,520
PDP-95,425
LP-179,917
NNPP-1655