Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa
Kai Tsaye: Zaben 2023 a Najeriya
Kai Tsaye: Zaben 2023 a Najeriya

Zaben 2023 a Najeriya

Ku kasance da VOA Hausa kai tsaye kan zaben Najeriya na 2023 a VOAHausa.com.

Zaben 2023: Buhari Ya Koma Daura Ana sa ran shugaba Buhari zai kada kuri’arsa a rumfar zabe da ke kusa da gidansa a garin Daura tare da mai dakinsa Aisha Buhari da sauran ahalinsa.

04:37 Maris 01, 2023

Tinubu Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa

Dan takarar jam’iyar APC, Bola Tinubu ya lashe zaben shugaban kasa bayan ya sami kashi 36% na kuri’un da aka kada a zaben shugaban kasa da aka gudanar ranar asabar, yayinda dan takarar jam’iyar PDP Atiku Abubakar ya zo na biyu da kashi 30% dan takarar Jam'iyar Labour Peter Obi kuma ya zo na uku da kashi.26%.

Tinubu ya doke sauran ‘yan takara goma sha takwas da kuri’u APC-8,794,726, yayinda dan takarar jam’iyar PDP Atiku Abubakar ya sami kuri’u 6,984,520, Peter Obi na jam’iyar Labour ya sami kuri’u 6,101,533, yayinda dan takarar jam’iyar NNPP-Rabi’u Musa Kwankwaso 1,496,687.

04:33 Maris 01, 2023

Sakamakon Zaben Shugaban Kasa

APC-8,794,726

PDP-6,984,520

LP-6,101,533

NNPP-1,496,687

02:37 Maris 01, 2023

Shugabanni Yammacin Afirka Sun Bukaci INEC Ta Kiyaye Dokar Zabe

Shugabanni a yankin yammacin Afirka sun bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da ta bi tanade-tanaden dokar zabe ta 2022 dangane da tattara sakamakon zaben shugaban kasa da na 'yan Majalisar dokokin kasar da aka gudanar a ranar Asabar.

Wakilan kungiyar dattawan Afrika ta Yamma (WAEF) ne suka yi wannan kiran a Najeriya, ciki har da tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan da tsohon shugaban Ghana John Mahama, a wata sanarwa da suka fitar jiya Talata a Abuja.

Shugabannin sun kuma yi kira da a kwantar da hankula a kasar, tare da yin kira ga INEC da ta magance matsalolin da masu ruwa da tsaki daban-daban suka gabatar dangane da harkokin zabe.

01:38 Maris 01, 2023

Yawan Jihohin Da Manyan Jam'iyu Su Ka Lashe

APC-12

PDP-12

LP-12

NNPP-1

Domin Kari

XS
SM
MD
LG