Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Gana Da Yan Najeriya Mazaunan Rwanda


shugaba Muhammadu Buhari
shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari , ya yaba wa matasan Najeriya da suka yi fice a gida da waje, inda ya ce kasar za ta yi maraba da kwarewarsu da jarin da za su zuba don bunkasar tattalin arziki.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun fadar shugaban kasa Femi Adesina ya fitar a ranar Asabar, Shugaban ya yi wannan jawabi ne a wani taro na ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje a gefen taron kungiyar shugabannin kasashe masu tasowa.

A jawabi da ya gabatar shugaba Buhari ya ce ‘‘Na yi matukar farin ciki da na kasance a birnin Kigali na kasar Ruwanda da kuma saduwa da ku, ’yan Najeriya mazauna kasashen waje a wani bangare na tarukan da nake yi da ’yan Najeriya a duk inda na kai ziyara wasu kasashe."

Buhari ya yabawa matashi dan Najeriya Yewande Adebowale, wanda ke cikin matasan da suka lashe gasar matasa na shekarar 2022 a Kigali.

Haka kuma yabawa Esther Olanrewaju da Favor Aderinto wadanda suka samu lambar yabo ta zama hazikan daliban Afirka, dake digirin digir-gir fasahar na'ura mai kwakwalwa da fannin koyan aikin lataroni.

shugaban ya nuna alfarinsa ga daliban da ma sauran matasan Najeriya da su ka yi fice a gida da waje.

Haka kuma ya bayyana kudurin gwamnati hada kan 'yan Najeriya gida da waje, don bunkasa tattalin arzikin kasar da kuma zaman lafiya da tsaro.

Buhari ya sha alwashin yin aiki tukuru don kare dukkan 'yan kasar a duk inda suke, don samin kwanciyar hankali da kuma samun cikakkiyar dama garesu don cimma ingantacciyar rayuwa.

Babbar jakadar Najeriya a kasar Rwanda, Ambasada Aishatu Musa, ta shaida wa shugaba Buhari cewa ‘yan Najeriya gaba daya suna da kyawawan halaye, kuma yawansu ya karu daga 100 zuwa 400 a shekarun baya-bayan nan, “kuma suna aiki fannoni daban-daban kamar su aikin banki da noma da fannin ilimi da sadarwa da dai sauransu.”

XS
SM
MD
LG