Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawan Najeriya Na Da Hurumin Bincikar Shugaban Kotun Da’ar Ma’aikata - Kotu


Shugaban Majalisar Dattawa ta 9, Ahmad Ibrahim Lawal
Shugaban Majalisar Dattawa ta 9, Ahmad Ibrahim Lawal

Wata babbar kotun tarayya da ke da zama a birnin Abuja ta ce Majalisar Dattawan Najeriya na da hurumin bincikar shugaban Kotun Da’ar Ma’aikata, Danladi Umar kan zargin cin zarafin wani mai gadi a wata kasuwa da ke unguwar Wuse na birnin Abuja.

Da ya ke yanke hukunci a ranar Talata, mai shari’a Inyang Ekwo, ya ce shugaban kotun CCT ya kasa nuna kyawawan dabi’u na mu’amala da jama’a ta hanyar halayensa, la’akari da cewa hukumar Da’ar Ma’aikata ta ginu ne kan wata doka da Majalisar Dokoki ta kasa ta amince da ita, don haka tana da hurumin bincikar halinsa.

Daga bisani ne kotun ta yi watsi da bukatar da Umar ya shigar da ke neman a dakatar da binciken da kwamitin Majalisar Dattawa dake kula da yanayin da’a, gata da kuma kararrakin jama’a, saboda rashin cancantar bukatar.

Shugaban Kotun Da'ar Ma’aikatar wato Danladi Umar, a wata kara mai lamba FHC/ABJ/CS/ 671/2021, yana kalubalantar ikon Majalisar Dattawa ta gudanar da bincike a kansa kan zargin da ake masa na cin zarrafin wani mai gadi a kasuwar Banex da ke birnin Abuja.

Idan ana iya tunawa, a karshen watan Maris na shekarar 2021 ne faya-fayen bidiyoyin da ke nuna yadda shugaban Kotun Da’ar Ma’aikatan Najeriya şato CCT, Danladı Umar, ya na cin zarafin wani maigadi a kasuwar Banex suka mamaye kafafen sada zumunta, lamarin da ya jawo suka da kiraye-kirayen a cire shi daga kan mukaminsa don bai dace da matsayin ba.

Rahotanni daga bangaren Danladi Umar sun yi nuni da cewa maigadin ya masa barazanar dukansa ne a yayin da yake kokarin faka motarsa a daidai gurin da ba a ajiye wata mota ba, shi ya sa ya mayar da martani ga maigadin.

Akwai lokacin da kwamitin Majalisar Dattawa ta bayyana cewa wanda ya shigar da karar ya janye ta.

Saidai a baya, da ya ke magana da manema labarai daga bisani, maigadin mai suna, Sagwak ya ce bai janye karar da ya shigar gaban majalisar ba, ya na mai cewa ya yi mamakin karantawa a shafukan jaridu cewa ya yi hakan.

Maigadin mai shekaru 22, ya yi zargin cewa Umar da dan sandan da ke da aiki tare da shi sun ci zarafinsa bayan ya sanar da shi Mal. Umar cewa bai kamata ya faka motarsa a gaban wani shago da ke Banex Plaza a ranar 30 ga watan Maris na shekarar 2021 ba.

Har yanzu dai ana dakon matakin gaba kan lamarin a gaban kotun.

Majiya: Channels TV.

XS
SM
MD
LG