Tuni har wasu daga gwamnonin, musamman a APC, su ka zabi daya daga cikin manyan masu neman tikitin jam’iyyar.
Dama ko da kada kuri'a za a yi a zaben fidda gwani, gwamnoni na da tasiri kan wakilan da akan tara don zaben.
Wannan ya sa manyan 'yan takarar ke zama da gwamnonin don neman goyon bayan su da hakan ke nuna samun goyon bayan gwamna tamkar samun jihar ce gaba daya.
Masanin harkokin siyasa Dr. Abubakar Kari ya ce ba lallai ne iyayen siyasa su hana mabiyansu fitowa takara ba don salon zaben 2023 na daban ne.
Kari na magana ne kan fitowar Osinbajo alhali ga maigidansa Tinubu na takarar.
Fadar gwamnatin ta bakin Garba Shehu ta ce sam ba a samu baraka a taron APC ba, inda sauran 'yan takarar fadar ba su samu nasara ba sai 'yan takarar gwamnoni.
Ba alamun za a yi zaben APC na fidda gwani da kada kuri’a in an duba yanda jam’iyyar ta karkata ga daidaitawa amma PDP ka iya zuwa ga kada kuri'a don barin kofar takara bude.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: