Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da Alama An Samu Rabuwar Kawuna Tsakanin Gwamnonin APC Gabanin Babban Taron Jam’iyyar


Wasu gwamnonin jam'iyyar APC(Facebook/APC)
Wasu gwamnonin jam'iyyar APC(Facebook/APC)

Alamu na nuna an samu rabuwar kawuna a tsakanin gwamnonin jam’iyayr APC 23 gabanin babban taron jam’iyyar a 26 ga watan nan.

ABUJA, NIGERIA - Wannan na zuwa bayan rudanin kwabewa ko akasin haka na gwamna Mai Mala Buni a matsayin shugaban rikon jam’iyyar na kara daukar sabon salo.

Zuwa yanzu ba bayani kai tsaye daga shugaba Muhammadu Buhari na nada gwamnan Neja Abubakar Sani Bello a matsayin wanda zai jagoranci jam’iyyar a babban taro, amma daya daga fitattun gwamnonin APC Nasir El-rufai ya ba da tabbacin shugaba Buhari ne ya kawar da gwamna Buni da hakan ya kawo gwamna Bello kan matsayin.

Muhammadu Buhari
Muhammadu Buhari

A zantawa da gidan talabijin na Channels El-rufai ya ce gabanin tafiyar da shugaba Buhari ya yi London don neman magani ya damka alhakin jam’iyar ga gwamnonin don tabbatar da an gudanar da babban taron kamar yanda a ka tsara.

El-rufai ya ce a bangaren su, su na da gwamnoni 19 cikin 23 da ke bayan gwamna Bello kuma za su tsaya kan sabon shugaban jam’iyyar ya fito daga arewa ta tsakiya duk da bai ambaci sunan Sanata Abdullahi Adamu kamar yanda a ke yayatawa ba, amma ya ce daidaitawa za a yi a fito da sunan mutum daya.

Gwamna El Rufai (Facebook/El Rufai)
Gwamna El Rufai (Facebook/El Rufai)

Masana siyasa na cewa duk wannan gwagwarmayar na da alaka da inda ‘yan siyasar su ke son kasancewa a babban zabe mai zuwa.

Sai dai mai taimakawa gwamna Buni ta layukan yanar gizo Haruna Sardauna ya ce sam ba su amince ko gamsu da cewa shugaba Buhari ya ba da wannan umurnin ba.

Yanzu zai yi wuya a dorar da wata magana mai karfi gabanin taron majalisar koli na jam’iyyar da a ke sa ran gabatarwa makwan gobe.

Saurari rahoto cikin sauti daga Nasiru Adamu El-Hikaya:

Alamu Na Nuna Cewa An Samu Rabuwar Kawuna Tsakanin Gwamnonin APC Gabanin Babban Taron Jam’iyyar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:42 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG