Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hanifa: Abin Da Wasu Masu Makarantun Kano Ke Cewa Kan Soke Lasisinsu


Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje
Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje

Wasu daga cikin mamallakan makarantun masu zaman kansu sun ce umarnin soke lasisin na su ya haifar da rudani.

Iyayen yara da dalibai da kuma mamallaka makarantu masu zaman kansu sun shiga rudani a jihar Kano, biyo bayan matakin gwamnatin jihar na soke lasisin dukkanin makarantun da ba na gwamnati ba. Sai dai kungiyar masu makarantun sun roki gwamnati ta yi adalci.

Wannan mataki na soke lasisin makarantu masu zaman kansu a Kano nada nasaba da abin tir da kyama wadda Kano ke alhinin sa na kisan gillar da Abdulmalik ya yiwa dalibar makarantar sa Hanifa Abubakar ‘yar shekaru 5, wanda jiya litinin ‘yan sanda suka gurfanar a gaban kuliya.

Yanzu haka dai masu makarantun a Kano na bayyana mabanbantan ra’ayi da fahimta dangane da wannan batu.

“A samu wani kwamiti mai karfi a ba shi nan da kwana goma zuwa sati biyu, gaba daya makarantun da suke jihar nan, daya bayan daya, a sake tantancewar da aka yi musu. Gaba daya an shiga rudu, iyayen yara a rude, malamai a rude, masu makarantu a rude.” In ji Hajiya Asma’au Yahya, Daraktar a Kwalejin Excel da ke Kano.

Ita kuwa, Hajiya Rabi Hussani Adamu tsohuwar kwamishinar ilimi a jihar Jigawa da ke zaman guda cikin mamallaka makarantun da aka sokewa lasisi na cewa mai yi wa aikin tantancewar ba zai dauki lokaci ba.

“Ina ga abin da suke nufi shi ne sai an tantance an ba da lasisi, kuma tantancewar nan, kila za su yi shi cikin gajeran lokaci, ta yadda ba zai shafi harkar ilimin yara ba. Ni a tawa fahimtar ba cewa aka yi a rufe ba” In ji Hajiya Rabi.

Amma kungiyar mamallaka makarantun da ba na gwamnati ba, ta yi jan hankali ga gwamnati. Hajiya Maryam Magaji ita ce mataimakiyar shugaban kungiyar ta kasa.

“In dai za a yi shi bisa adalci, a bincika makarantun nan, kuma za a tsaya a yi abin da ya kamata, a bincika makarantun nan wadanda suke da matsaloli a fitar da su, wadanda ba su da matsaloli, don Allah don Annabi kada gwamnati ta saka su a cikin matsala.” A cewar Hajiya Maryam.

Sai dai kungiyoyin tallafawa ilimi a Najeriya na ganin sakaci da aikin bibiya daga hukumomin gwamnati ne ya haifar da wannan yanayi.

Comrade Sufyanu Bichi na Cibiyar tallafawa ilimin ‘yaya mata ta Girls Education Partnership ya ce inda aka kaucewa hanya shi ne wajen rashin bin tsarin yadda ake daukan malamai a aiki da yadda za a rika ba su ilimi.

Ya kara da cewa akwai tsarin ziyarar makarantu da ake yi a da duk shekaru uku don ganin halin da suke ciki, yana mai cewa amma a yanzu a yi watsi da tsarin.

Cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, Sakataren yada labaran gwamnati, Abba Anwar ya ce Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce suna kan duba lamarin.

XS
SM
MD
LG