Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Ta Nuna Sha'awar Saka Jari a Najeriya


Taron inganta dangantakar kasuwanci tsakanin Najeriya da Rasha
Taron inganta dangantakar kasuwanci tsakanin Najeriya da Rasha

A kokarin inganta dadaddiyar danganta dake tsakanin Najeriya da kasar Rasha, cibiyar kasuwanci da masana’antu tare da hadin kwiwar kungiyoyin yan’kasuwa na ma’adinai da albarkatun noma a Najeriya sun karbi tawagar yan’kasuwa da masa’antun kasar Rasha wadanda suka nuna sha’awarsu ga fannonin daban daban na tattalin arzikin Najeriya da za su iya juba jari.

Ana sa ran wannan dangatakar za ta haifar da da mai ido tsakanin kasashen biyu a fannoni da dama mussaman ta fannin cinikayya da raya masana’antu da kuma samar da ayyukan yi wadda jigo ne wajen kawo zaman lafiya idan aka yi la’akari da kalubalen da Najeriya ke fuskanta

Farfesa Abdullahi Shehu Jakadan Najeriya a kasar Rasha
Farfesa Abdullahi Shehu Jakadan Najeriya a kasar Rasha


Farfesa Abdullahi shehu shi ne jakadan Najeriya a Rasha kuma shi jagoranci tawagar ya fadi cewar ''an gudanar da tattauna daki daki a fannoni daban daban wadanda suka shafi harkokin man fetur da iskar gas, harkokin noma mussaman samar da kayyakin aiki da kuma harkokin sarrafa ma'adinai da samar da fasaha da kimiya wajen inganta tsaro a guraren jiragen kasa da na sama wadannan wurare ne da mutanen Rasha su ka kware akai kuma muna kyautata zaton yan kasuwan Najeriya za su amfana daga irin kimiyar da Rasha ta ke da shi, dan haka idan su ka zo Najeriya samu samu danganta mai inganci''

Muhammad Yusuf Lere babban mamba ne a cibiyar inganta harkokin kasuwanci a Najeriya ya ce wannan babbar dama ce ga dukkan kasashen biyu tare da kari kan cewa yawan kamfanonin da suka zo ya nuna cewa Najeriya ta na da abun da zata bayar

Daya daga cikin shugabanin kamfanin Metalwork dake da abubuwa daban daban da ke kerawa a kasar rasha Ivan Klevtsov wanda kuma shi ne shugaban tawagar kamfanonin da suka zo Najeriya ya bayyana cewa

‘’Najeriya na da yanayi na kasuwanci mai kyau kuma sun samu fahimta da yan kasuwa dan ba za mu iya aiki ba su ba, mu na sa ran wakiltar sauran yan kasuwan daga Rasha a Najeriya.’’

Paterson Bana wanda ya samu halartar taron ya shaida cewan wannan babban dama ce ta tada tsohuwar dangantaka tsakanin kasashen biyu kuma yana fatan wannan zai toshe dukkan wani gibi da aka samu a baya.

Kwararru da dama sun nuna cewar yunkurin da aka yi a wannan karon da kyakyarwar niyar da ake da shi ana sa ran ba zai kare a taron shan shayi kamar yadda akan yi baya ba.

Saurare cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:27 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG