Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisa Ta Dakatar Da Shirin Kara Kudin Wutar Lantarki a Najeriya - 2'16"


please wait

No media source currently available

0:00 0:02:16 0:00
Majalisar Dattawan Najeriya ta umarci kamfanonin rarraba wutar lantarkin kasa da su dakatar da shirin karin kudi da suka yi niyyar farawa a yau Laraba.

Karin kudin da Kungiyar Kamfanonin rarraba wutar lantarki ta ce za ta yi daga yau 1 ga watan Yuli, ya gamu da fushin ‘yan Majalisar Dokokin kasar ne inda ‘yan majalisar dattawa suka ce akwai abin dubawa.

Sanata Sahabi Ya'u wanda shi ne mataimakin mai tsawatarwa a majalisar dattawa ya ce yanzu tattalin arzin duniya ya karye saboda annobar cutar korona kuma a yanzu gwamnatin na neman abin da za a ci ne ba abin da za a dora wa talaka nauyi ba.

Sahabi Ya'u ya ce batun karin kudin wuta bai dace a yanzu ba.

A lokacin da yake nazari akan batun karin kudin wutar lantarki Sananta Mai wakiltan Katsina ta Arewa Sanata Ahmed Babba Kaita ya ce kamfanonin ba su da hujjar yin karin kudi akan abin da ba sa bayar ba.

A cewarsa, ba a samun wutar lantarki kamar yadda ya kamata a kasa, kuma kamfanonin sun gaza kawo mitoci da zai sa mai sayen wuta ya san yawan wutar da ya sha kafin ya biya,

Amma Shugaban sashin hulda da Jama'a na Kamfanin rarraba wuta na Kaduna Abdulaziz Abdullahi ya ce kudin wuta yadda ake sayar da shi ba daidai yake da kudin da aka saye shi ba.

Saboda haka ne gwamnati ta ba da izinin yin karin amma kuma ta ce za a yi karin kudin da sharadi, na cewa dole ne a samar wa mai sayen wuta yawan wutar da yake so a lokacinda ya ke so.

Ya kara da cewa, tun watanni ukun baya aka so a yi karin kudin wutar amma bullar cutar korona ce ta hana a yi.

Sai dai Sanata Ahmed Babba Kaita ya ce gwamnati tana kokarin ganin an magance matsalar wutar lantarki ne gaba daya, amma bai ga dalilin da zai sa mutum ya sayi kamfanin ba da wuta kuma bai iya bayar da wutar ba.

Ya kara da cewa, idan har kamfanonin ba za su iya ba, to su saki kamfanonin wasu su saya.

Majalisar ta ce ba za su yarda a ta da maganar karin kudin wutar lantarki ba har sai tsakiyar shekara mai zuwa idan abubuwa sun lafa a kasa.

XS
SM
MD
LG