Yan sanda sun harba barkonon tsohuwa ga dubban masu zanga-zanga da suka taru a kan tituna ranar Lahadi a Khartoum, babban birnin kasar da wasu yankunan don yin wannan zanga-zangar wadda ita ce ta farko tun wadda aka yi a watan Yuni da aka samu mace-macen mutane yayin murkushe zanga-zangar. An samu rahotannin gudanar da wasu zanga-zanga a jiya Litini.
Anan Washington, Amurka ta yi Allah-wadai da irin harin da ake kaiwa fararen hular wannan kasar.
Ma’aikatan harkokin wajen Amurka ta fadawa Muryar Amurka cewa “jami’an tsaron Sudan sun hallaka jama’a da yawa da suke zanga-zangar lumana, ya kuma kamata a kama su da laifin kisan da su ka yi wa fararen hula.”
Facebook Forum