A cigaba da fafatawa da akeyi a gasar wasannin cin kofin kwallon kafa ta zakarun turai (UEFA ) 2018/19 a matakin wasan rukuni zagaye na hudu.
A yau kungiyoyi 16 zasu kece raini inda Crevna na kasar Serbia zata karbi bakuncin Liverpool na kasar Ingila, da misalin karfe 6:55 na yammaci agogon Najeriya da Nijar, sai Monaco, da Club Brugge.
Da misalin karfe 9 na yammaci kuwa Inter Milan zata karbi bakuncin Barcelona, ne a kasar Itali, Atletico Madrid suna tare da Borussia Dortmund, sai Napoli da Paris-saint German.
A Sauran wasannin kuwa Tottenham Hotspur na kasar Ingila zasu fafata da PSV dake Netherlands FC Porto su barje gumi da Lokomotiv Moscow, na kasar Rasha.
Schalke 04 zasu kece raini tsakaninsu da Galatasaray na kasar Turkiya. A wasu labaran kuwa tsohon kocin Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Arsene Wenger, na daf da kama aiki a Kungiyar kwallon kafa na AC Milan dake kasar Itali a matsayin mai horas da 'yanwasa.
Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona da Manchester United sunjera sahu guda wajan zawarcin matashin danwasan Benfica mai shekaru 15 mai suna Ronaldo Camara, wanda yake buga wasa wa tawagar 'yan kasa da shekaru 17 na kasar Portugal.
Kocin Tottenham Mauricio Pochettino yaba magoya bayan Kungiyar hakuri game da rashin kammala aiki filin wasanta da ba'ayi ba, Tottenham dai a yanzu haka tana buga wasannin tane a filin wasa na Wembley sakamakon rashin kammala aiyukanta.
Inda a yanzu ake ganin kafin ta shiga sabon filin nata ka iya kaiwa watan Janairu 2019 mai zuwa.
Facebook Forum