Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Wasa Lionel Messi Zai Taka Leda A Gasar Zakarun Turai Gobe


Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta sanya sunan Lionel Messi a cikin tawagar kungiyoyin wasan kwallon da zasu kece raini da Inter Milan, ranar Talata a gasar cin Kofin zakarun Turai, matakin wasan rukuni, duk ko da raunin da Messi ya samu na karaya a hannunsa makwanni biyu da suka shude.

Bayyana sunan Messi a cikin wannan tawagar ya zo da bazata, ganin yadda a farko aka yi hasashen cewa, mafi karancin lokacin da zai shafe yana jinya ya kai tsawon makwanni uku kafin ya dawo fagen taka leda.

Sai dai tun a makon jiya, anga dan wasan ya fita filin atisayen Kungiyar ta Barcelona wanda ba a yi tsammanin zai yi gaggawar fara buga wasa ba.

Messi bai samu damar buga wasan da Kungiyar ta Barcelona ta lallasa abokiyar hamyyarta Real Madrid da kwallaye 5 da 1 ba, a wasan La Liga, mai taken El-Classico, haka kuma wasan da suka samu nasara akan Inter Milan da ci 2 da 0.

Messi ya sami karaya ne a wasan da kugiyarsa ta doke ta Sevilla da kwallaye 4 da 2. Kocin kungiyar yace ko da dan wasan bai samu damar fafata wasan da Inter Milan a kasar Italiya ba, to ba shakka zai buga wasan da kungiyar za tayi da Real Betis nan gaba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:46 0:00

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG